’Yan bindiga sun harbe ’yan sanda biyu a Katsina

An yi musayar wutar ce a Kauyen Baure na Karamar Hukumar Safana.

’Yan bindiga sun harbe ’yan sanda biyu a Katsina

Ana fargabar mutuwar wasu jami’an ’yan sanda biyu da karar kwana ta cimmasu yayin artabu da ’yan bindiga a Jihar Katsina.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Sanusi Buba ne ya tabbatar da hakan yayin gana wa da manema labarai a Babban Ofishin ’Yan sanda da ke Birnin Katsinan Dikko.

CP Buba ya ce ASP Yakubu Joshua da Sajen Zaharadden Yuguda ne ’yan sandan biyu da suka riga mu gidan gaskiya a yammacin ranar Alhamis yayin artabu da wasu ’yan bindiga masu satar shanu da garkuwa da mutane.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, artabun da aka rika musayar wuta tsakanin jami’an ’yan sanda da ’yan bindigar ta gudana ne a Kauyen Baure da ke Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.

Bayan faruwar lamarin ne Kwamishinan ya umarci wata tawaga bisa jagorancin Mataimakinsa Mai Kula da Shiyyar Dutsinma, ACP Aminu Umar zuwa maboyar ’yan bindigar.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi wata musayar wuta tsakanin bangarorin biyu inda aka kashe wasu ’yan bindiga biyu yayin da ragowar suka tsare suka bar makamai masu tarin yawa ciki har da bindigogi kirar AK 47 da kuma kwanson alburusai.

Kwamishinan ya nemi jama’a da su ci gaba da taimaka wa hukumomi da rahoton duk wani motsin da ba su amince da shi ba musamman ire-iren maboyar wadannan barayi.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa za su ci gaba da zage dantse wajen yakar duk wasu masu tayar da zaune tsaye domin su fuskanci fushin doka daidai da abin da suka aikata.