’Yan bindiga sun harbe ’yan sanda uku

Sun kona motar ’yan sanda a Kaduna ’Yan bindiga da ba a san su wane ne ba sun harbe ’yan sanda uku da ke aiki a shingen duba ababen hawa da ke tsakanin Fadan Karshi zuwa Saboke a Karamar Hukumar Sanga da ke Jihar Kaduna. Wani ganau a yankin ya shaida wa Aminiya cewa maharan […]

’Yan bindiga sun harbe ’yan sanda uku

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kaduna, Ali A. Janga

  • Sun kona motar ’yan sanda a Kaduna

’Yan bindiga da ba a san su wane ne ba sun harbe ’yan sanda uku da ke aiki a shingen duba ababen hawa da ke tsakanin Fadan Karshi zuwa Saboke a Karamar Hukumar Sanga da ke Jihar Kaduna.

Wani ganau a yankin ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun bude wuta ne da isarsu wajen inda direban motar ’yan sandan ya sha da kyar bayan ya gudu zuwa cikin daji.

Lamarin na zuwa ne jim kadan da kaddamar da karamin barikin sojoji a garin Gwantu, hedkwatar Karamar Hukumar Sanga don inganta harkokin tsaro a yankin.

Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Sanga Alhaji Abubakar Abba Umar ya tabbbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kwashe gawarwakin ’yan sandan zuwa babban asibitin Gwantu. Ya ce ’yan sanda biyu sun mutu ne nan take yayin da na uku ya cika a hanyarsu ta zuwa asibiti.

Ya koka kan yadda kashe-kashe ke dada kamari a yankin inda ya yi kira ga jami’an tsaro su kara kaimi wajen dakile ayyukan ’yan bindiga a yankin.

A wani labarin wadansu ’yan bindiga sun kone wata motar ’yan sanda masu rakiya hari har suka konata a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Wata majiya a yankin ta shaida wa Aminiya cewa ’yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 12 na rana lokacin da motar ke kan hanyarta ta zuwa Kaduna a kusa da Kwaru a kusa da garin Udawa.

Motar kirar Hilud ’yan ta’addan sun harbi dan sanda daya a cikin motar da dan banga daya amma ba su rasu ba, an kai su asibiti domin jinya.

Mukaddashin Kakakin ’Yan sandan Jihar ASP Sulaiman Abubakar bai amsa waya ba sannan bai ba da amsar sakon tes da aka masa ba don neman karin bayani.