’Yan bindiga sun harbe ’yan sanda uku a Bauchi
Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun harbe ’yan sanda uku da ke aiki a shingen duba ababen hawa a kusa da garin Tilden Fulani a karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi a karshen mako.Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa ’yan sanda biyar ne ke aikin a […]
Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun harbe ’yan sanda uku da ke aiki a shingen duba ababen hawa a kusa da garin Tilden Fulani a karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi a karshen mako.
Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa ’yan sanda biyar ne ke aikin a wurin, amma sai biyu daga cikinsu suka shiga gari domin sayen abinci, sai ’yan bindigar suka bude wa sauran ukun wuta daga bisani suka arce da makamansu.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne lokacin da ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya. Kuma wasu majiyoyin tsaro sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 zuwa 11:30 na dare.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Haruna Muhammed ya tabbatar wa wakilinmu da faruwar lamarin sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.