’Yan bindiga sun harbi likita, sun sace mutum 5 a asibiti a Katsina

Wannan shi ne karo na uku da mahara ke kai wa asibitoci hari a jihar.

’Yan bindiga sun harbi likita, sun sace mutum 5 a asibiti a Katsina

’Yan bindiga sun kai hari a Asibitin Gwamnati da ke garin Kankara, Jihar Katsina, inda suka harbe wani likita tare da sace mutum biyar.

Harin ya faru ne a daren ranar Talata, inda ’yan bindigar suka harbi wani likita mai suna Dokta Murtala Sale Dandashire, sannan suka yi garkuwa da mutum biyar a cikin asibitin.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ya tabbatar da faruwar harin a daren Talata.

Ya ce: “A daren jiya, ’yan bindiga sun kai hari Asibitin Gwamnati da ke Ƙankara, a Jihar Katsina. Sun harbi Dokta Murtala Sale Dandashire, sannan suka sace mutum biyar a cikin asibitin.”

majiyar ta kara da cewa wannan shi ne karo na uku da aka kai hari a wasu asibitocin jihar cikin watanni uku da suka gabata.

A baya, wasu mahara sun taba kai hari Asibitin Gwamnati da ke Kurfi da Asibitin Mai Tsani da ke karamar hukumar Dutsin-ma.

Dokta Murtala Sale Dandashire, wanda ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Kankara, ya kasance likitan da ya fi kowa kwazo a shekarar 2019 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar, Abubakar Sadiq Aliyu, ya ci tura, domin ba a samun sa a waya da safiyar Laraba ba.