’Yan bindiga sun huce fushi kan masu ba wa jami’an tsaro hadin kai

Wannan hukunci ne a sakamakon bai wa jami’an tsaro bayanai a kansu da suke yi.

’Yan bindiga sun huce fushi kan masu ba wa jami’an tsaro hadin kai

’Yan bindiga

’Yan bindiga sun kashe wasu mutane biyar mazauna garin Rogoji da ke Karamar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara a wani hari da suka kai a karshen wannan mako.

Da suke tabbatar da wannan al’amari, mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun yi musu aika aikar ne a matsayin hukunci, sakamakon bai wa jami’an tsaro bayanai a kansu da suke yi.

RFI ya ruwaito cewa garin Rogoji na da nisan kilomita 2 ne kawai daga kwaryar garin Bakura.

Majiyoyi sun ce mazauna garin sun taimaka wa jami’an tsaro da ‘yan banga sosai a wajen yaki da ‘yan ta’addan da suka hana su sakat a yankunan Lambar Bakura da Dogon Karfe.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun shiga garin ne da safiyar Alhamis a lokacin da al’umma ke shirin sallar asuba, duk da turjiya da suka gamu da ita, inda suka kashe mutane 5.