’Yan bindiga sun kai hari a sansanin soji a Katsina
Sansanin sojin yana Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Shimfida inda aka kashe soja daya da jami’in NSCDS daya nan take suka jikkata wasu
‘Yan bindiga
’Yan bindiga sun kashe wani soja da wani jami’in Rundunar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) a wani hari da ’yan bindigar suka kai wani sansanin soji a Jihar Katsina.
Wani ganau ya shaida mana a ranar Alhamis cewa dandazon maharan da suka kai harin da misalin karfe 10 na dare, sun bude wuta babu kakkautawa a kan sansanin da ke yankin Shimfida a Karamar Hukumar Jibia ta jihar.
- Kashi 90 cikin 100 na gwamnoni ba su cancanci shugabanci ba
- Iyaye sun yi wa malamin dansu dukan tsiya
Ya kara da cewa jami’an tsaron da aka raunata a harin suna asibiti ana ba su kulawa.
Mai Magana da Yawun Hukumar NSCDC a Jihar Katsina, DSC Muhammad Abdara, ya tabbatar da rasuwar jami’in hukumar a harin, amma ba mu samu sojoji ba domin ji daga bangarensu.
Idan ba a manta ba, a watan Satumban 2021, ’yan bindiga sun yi wa ayarin wasu sojoji kwanton bauna a yankin inda suka kashe soja uku suka kuma jikkata wasu da dama.