’Yan bindiga sun kai hari coci a Kaduna

Sai dai Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da masu ibada da dama.

’Yan bindiga sun kai hari coci a Kaduna

Akalla mutum daya ya mutu bayan harin wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne a kan wata coci dake yankin Karamar Hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan harin da aka kai da safiyar ranar Lahadi, a daidai lokacin da mutane suke tsaka da ibada.

Sai dai Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da masu ibada da dama, yayin da wasu kuma suka ji raunuka.

Karamar Hukumar Chikun dai ta jima tana fuskantar hare-haren ’yan bindiga kuma duk wani yunkuri na shawo kan matsalar ya ci tura.

Ko a ranar Talatar da ta gabata sai da aka kai hari Jami’ar Greenfield dake cikin Karamar Hukumar kuma aka sace dalibai da dama, kafin daga bisani a tsinci gawar uku daga cikinsu ranar Juma’a.

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato