’Yan bindiga sun kai hari da kashe manoma 23
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa da farko ’yan bindigar sun haura ta ƙauyen ne da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar ranar Laraba ba tare da sun harbi kowa ba.
Sama da manoma 23 aka ruwaito cewa, ’yan bindiga sun kashe su a unguwar Sauna/Ruwan Gora da ke Ƙaramar Hukumar Talata Mafara a Jihar Zamfara.
Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a ɓoye sunansa yayin da yake magana da jaridar Daily Trust, ya bayyana cewa da farko ’yan bindigar sun haura ta ƙauyen ne da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar ranar Laraba ba tare da sun harbi kowa ba.
- Gobara ta lalata kayan miliyoyin Naira a coci
- An yi wa wata mata ɗaurin wata 6 kan aikata damfara a Borno
“ ’Yan bindigar sun bi ta ƙauyenmu da misalin ƙarfe 2:00 na rana ba tare da sun cutar da kowa ba. Har ma mutane suna ƙirga adadin baburan da suke kansa,” in ji ɗan garin.
Ya bayyana cewa, daga baya maharan sun sake dawowa inda suka buɗe wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta, suna bin waɗanda suka yi ƙoƙarin tsira da gudu. “Sun kashe mutane 23. Suka kai musu hari a gonakinsu daban-daban, suka bi waɗanda suka gudu domin tsira suka kashe su,” in ji shi.
A cewar majiyar, ana tsaka da gudanar da shirye-shiryen birne gawarwakin mutane 23 a wuri guda a ranar Alhamis. “Mun haɗa gawarwakin mutane 23 ɗin domin birne su a lokaci guda a yau,” in ji shi.
Mazauna yankin sun yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da kuma Gwamnatin Tarayya da su hanzarta ƙarfafa tsaro a yankin domin kare rayuka da dukiyoyi.
“Idan aka ci gaba da kashe manoma da sace su, tabbas Jihar Zamfara za ta fuskanci ƙarancin abinci,” in ji shi.
Wani mazaunin garin daban, shi ma wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi iƙirarin cewa adadin waɗanda suka mutu na iya kaiwa 25, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da ƙoƙarin tantance ainihin adadin waɗanda harin ya shafa.
“ ’Yan bindigar sun sake dawowa suka kai hari a ƙauyen da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin jiya. Har yanzu muna tattara sunaye da kuma neman waɗanda suka rasa rayukansu,” in ji shi.