’Yan bindiga sun kai hari Damagun a karo na biyu
Wasu ’yan bindigar da ake kyautata zaton ’yan kungiyar BOKO HARAM ne, sun kai farmaki garin Damagum, fadar karamar Hukumar Fune, cikin Jihar Yobe, yadda suka tarwatsa jami’an tsaron JTF da ke garin tare da lalatagine-ginen gwamnati da dama hade da na’urar aika sakonni ta kamfanin sadarwar mallakar AIRTEL amma ba su samu kashe ko […]
Wasu ’yan bindigar da ake kyautata zaton ’yan kungiyar BOKO HARAM ne, sun kai farmaki garin Damagum, fadar karamar Hukumar Fune, cikin Jihar Yobe, yadda suka tarwatsa jami’an tsaron JTF da ke garin tare da lalata
gine-ginen gwamnati da dama hade da na’urar aika sakonni ta kamfanin sadarwar mallakar AIRTEL amma ba su samu kashe ko da mutum guda ba.
Wata majiyar da ke garin ta bayyana wa Aminiya kan cewar wadannan maharan sun zo garin ne a ranar Jumu’ar da ta gabata da wajen misalin karfe 6.00 na yamma, lokacin da mutanen garin ke shirin fara Sallar Magariba a kan motoci kusan bakwai ba babura masu yawa. Da zuwan su sai suka fara far wa tsohon ginin sakatariyar karamar hukumar, inda nan take suka banka wuta a wani sashinta, daga nan sai suka wuce ya zuwa mazaunin jami’an tsaron JTF suka far musu.
Wani mazaunin garin na Damagum da ya nemi da a saya sunansa ta wayar tafi da gidanka ya shaida wa Aminiya cewa, maharan bayan da suka samu tarwatsa tungar jami’an tsaron sai nan take suka banka wuta a mazauninsu, daga nan kuma suka tsallaka babban ofishin ’yan sandan garin da ke gab da mazaunar jami’an tsaron na JTF; nan ma suka banka masa wuta. A baya ma sun taba kona wannan ofishin, a wani harin da suka kawo garin amma aka sake gina shi.
Malamin ya ci gaba da cewar, lokacin da maharan suka shigo garin sun fada wa mutanen garin cewa, su bi a hankali kar su ji rauni, domin ba wurinsu suka zo ba; ba ruwansu da mutanen gari sun zo ne wurin jami’an tsaro. Shi ne mutanen garin daga bisani kowa ya shige gidansa amma kuma a tsorace, domin tsananin karar harbe-harbe da kuma tashin bama-bamai babu kakkautawa har wajen karfe 9.00 na dare, da suka ji komai ya yi tsit, wanda hakan ya nuna musu cewa da alama ’yan bindigar sun sulale.
Maharana, a cewarsa sun fasa shaguna sun kwashi kayayyakin abinci da abin sha da kuma magunguna, sun tsere da su tare da wasu motoci biyu na mutanen garin.
Wannan hari da ’yan bindigar suka kawo garin na Damagum dai shi ne, irinsa na biyu da suka taba kai wa garin kuma hari ne da ya zo kasa da wata guda da ’yan bindigar suka kai garin Damaturu, inda aka rasa rayukan mutane sama da 100.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin bangaren jami’an tsaro ko kuma wani jami’in karamar hukumar, lamarin ya ci tura.