’Yan bindiga sun kai hari ga yayan Gwamna Al-Makura
A ranar Asabar da ta gabata ce wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai hari gidan yayan Gwamnan Jihar Nasarawa kuma Mai martaba Sarkin Kwandare Alhaji Amadu Al-Makura da ke kan hanyar Shendam a Lafiya fadar jihar. Kodayake ’yan bindigar ba su yi nasarar harbin Sarkin ba, amma […]
A ranar Asabar da ta gabata ce wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kai hari gidan yayan Gwamnan Jihar Nasarawa kuma Mai martaba Sarkin Kwandare Alhaji Amadu Al-Makura da ke kan hanyar Shendam a Lafiya fadar jihar.
Kodayake ’yan bindigar ba su yi nasarar harbin Sarkin ba, amma sun harbi dogaransa biyu a lokacin harin.
Da yake ganawa da manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata, Sarkin ya gode wa Allah da Ya tserar da ransa a lokacin harin. Ya ce “Wadannan ’yan bindiga ba mu san ko su wane ne ba. Kuma ban taba tunani cewa irin wannan lamari zai faru da ni ba, saboda ba na gaba da kowa, kuma ba na fada da kowa, a iya sanina.”
Sarkin ya ce “Da misalin karfe 7:30 na dare bayan mun idar da Sallar Magariba, muna cikin masallacin da ke gidana sai kawai muka ji harbe-harben bindiga ta ko’ina a cikin gidana. ’Yan bindigar suna harbi suna cewa: “Ina Sarkin? Ina Sarkin?” Daga nan sai suka kewaye mu a masallacin suka ce kowa ya kwanta. Da jin haka sai na ja jiki na bar wurin. Kuma ba su dauki komai ba a gidana ba, haka a masallacin, sai dai wayar salulata kawai suka dauka suka tafi da ita. Ni dai idan akwai wanda yake tunani cewa ina gaba da shi ban sani ba. Ba na fada da kowa, sai dai watakila akidata ta gaskiya ne wani ba ya so, ya sa ya turo min wadannan mahara don su kashe ni, don ni mutum ne da duk abin da ka aikata idan ka zo gabana zan gaya maka gaskiya ko ka so, ko ka ki.”
Ya jinjina wa ’yan sandan da sauran jami’an tsaro game da yadda suka iso gidansa cikin gaggawa duk da dai ba su iske maharan ba. Ya ce ’yan bindigar suna tafiya bai kai minti biyar ba jami’an tsaro suka shigo gidansa ciki har da DPO da kuma Kwamishinan ’Yan sanda.
Da wakilinmu ya ziyarci dogaran Sarkin biyu da aka harba da ke jinya a wani asibiti da ke Lafiya ya lura sun fara samun sauki kamar yadda wani babban likitan asibitin ya tabbatar masa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa DSP Idrisu John Kennedy ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce maharan sun yi amfani da wata mota kirar Gulf ne suka ce su baki ne. A cewar sanarwar da ’yan bindigar suka yi yunkurin shiga gidan Sarkin sai dogaran biyu suka hana su. Daga nan ne sai suka fara bude wuta inda suka harbe su.
Rundunar ta yi kira ga duk wanda yake da bayyani game da wannan jar mota kirar Gulf da kuma ’yan bindigar ya yi maza ya shaida wa ofishin ’yan sanda mafi kusa don daukar mataki cikin gaggawa.
Jama’a sun yi ta yin tururuwa zuwa gidan Sarkin daga ciki da wajen jihar don yi masa jaje, cikin har da Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura wanda ya bayyana aukuwar lamarin a matsayin mummuna. Ya kuma roki Gwamnatin Tarayya ta inganta yanayin tsaro a jihar don dakile ayyukan batagari. Ya tabbatar wa Sarkin cewa gwamnatin jihar da hadin gwiwar jami’an tsaro za su binciko su kuma kamo wadanda suka kai harin don hukunta su.
Daga nan sai ya nanata cewa gwamnatinsa za ta tabbatar cewa ta aiwatar da rahoton kwamitin binciken rikicin Ombatse, domin hukunta wadanda ke da hannu a kisan jami’an tsaro a kauyen Alakyo a bara. Ya yi kira ga al’ummar jihar su cigaba da zaman lafiya da junansu, kuma gwamnatinsa ashirye take ta hukunta duk wanda aka kama yana ta da zaune tsaye.