‘Yan bindiga sun kai hari gidan Sanata a Bayelsa

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin na haya ne, sun kai hari gidan tsohon Sanata mai wakiltar gabashin Bayelsa, Sanata Nimi Barigha-Amange a gidansa da ke unguwar Ekeki, a Yenogoa babban birnin jihar. Tsohon Sanatan wanda ya wakilci yankin a shekarar 2007 zuwa 2011 a karkashin Jam’iyyar PDP, yana daga cikin makusantan tsohon Shugaban Kasa, […]

‘Yan bindiga sun kai hari gidan Sanata a Bayelsa

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin na haya ne, sun kai hari gidan tsohon Sanata mai wakiltar gabashin Bayelsa, Sanata Nimi Barigha-Amange a gidansa da ke unguwar Ekeki, a Yenogoa babban birnin jihar.

Tsohon Sanatan wanda ya wakilci yankin a shekarar 2007 zuwa 2011 a karkashin Jam’iyyar PDP, yana daga cikin makusantan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Ebele Jonathan.

Wani wanda ya nemi a sakaye sunan shi ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, inda ‘yan bindigan suka shiga gidan tsohon Sanatan.

Shima Sanatan, da yake Magana da manema labarai a ranar Laraba, ya ce har yanzu bai san ko daga ina aka turo maharani ba.

“Yan Bindigar sun yi zaton nazo gida a motata, don haka suka yi yunkurin aiwatar da mummunan aikinsu a kaina. Sun hauramin gida sanye da takunkumi a fuskokinsu”

“Yayin da suka tabbatar bana cikin motar sai suka bincike ko ina na gidan sannan suka tafi.” In  ji tsohon Sanatan.