’Yan bindiga sun kai hari gidan yarin Kalaba

Maharan kuma kashe ma’aikatan gidan daya

’Yan bindiga sun kai hari gidan yarin Kalaba

Gidan gyaran hali na Kalaba

Wasu mahara da ake kyautata zaton yan bindiga ne a ranar Laraba sun kai hari gidan gyaran hali na Afokang da ke Kalaba babban birnin Jihar Kuros Riba.

Rahotanni sun ce yayin harin, mutanen sun kashe daya daga cikin ma’aikatan da ke gadin gidan.

Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a jihar, Affanga Etim, ne ya tabbatar wa Aminiya afkuwar hakan a ranar Alhamis.

Sai dai Etim ya ce duk da hakan babu ko daya daga cikin mutanen da ake tsare da su a gidan da ya sami tserewa.

Ya ce, “Lokacin da ’yan ta’adan suka kai harbin kan mai uwa da wabi suka fara yi domin tsoratar da mutane da kuma ma’aikatanmu don su ci gaba da abin da ya kawo su.

“Da ganin haka sai jami’anmu suka mayar da martani. Ana cikin wannan musayar wutar ne suka harbe mana wani jami’i daya mai mukamin ASC daga baya kuma suka fara harbin jami’anmu.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai an kara tura jami’an tsaro gidan gyara halin na Kalaba domin kara karfafa tsaro a gidan.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa akwai tsagerun yankin da suke tsare da su a gidan wanda hakan ne ya sa tsagerun yankin masu fafutukar kafa kasar Ambazoniya suke barazanar fitar da ’yan uwansu daga ciki.

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda