’Yan bindiga sun kai hari Jami’ar Greenfield a Kaduna

Har yanzu ba’a a tabbatar da adadin daliban da suka sace ba.

’Yan bindiga sun kai hari Jami’ar Greenfield a Kaduna

Jami’ar Greenfield

Rahotanni daga Jihar Kaduna sun ce wasu gungun ’yan bindiga sun kai hari kan jami’ar Greenfield da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka sace dalibai da dama.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 10.30 na daren Talata, inda maharan rike da makamai suke harbe wani mai gadi daya a jami’ar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da sace daliban, sai dai ya ce har yanzu ba’a san adadin daliban da ’yan bindigar suka diba ba.

Ya ce ana ci gaba da kidaya domin tatance hakikanin adadin daliban da maharan suka sace.

Jalige ya ce cikin gaggawa ’yan sanda da sojoji suka yi wa makarantar tsinke bayan samun rahoton harin da aka kai, sai dai ba su yi sa’ar tarar da maharan ba wanda tuni sun kama gabansu.

Ya yi furcucin cewa za su yi wa al’umma karin haske da zarar sun samu tabbaci kan adadin daliban da aka sace.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan hari na zuwa ne bayan kwanaki kimanin arba’in da aukuwa makamancinsa, inda wasu ’yan bindiga suka kai hari makarantar horas da ayyukan noma da gandun daji da ke Mando suka sace dalibai mata zalla guda 39.

Na ƙi biyan kuɗin fansar ’yan uwana sun kuɓuta — Gwamnan Zamfara

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro