‘Yan bindiga sun kai hari kasuwar dabbobi a Taraba
Wasu ‘yan bindiga sun far wa kasuwar dabbobi da ke garin Mararrabar Kunini a Karamar Hukumar Lau ta Jihar Taraba. Wani shaidar gani da ido, ya bayyana cewa shi ma da kyar ya tsira da ran sa a wannan hari kamar yadda jaridar yanar gizo Premium Times ta ruwaito. “Maharan sun far wa kasuwar ne […]
Wasu ‘yan bindiga sun far wa kasuwar dabbobi da ke garin Mararrabar Kunini a Karamar Hukumar Lau ta Jihar Taraba.
Wani shaidar gani da ido, ya bayyana cewa shi ma da kyar ya tsira da ran sa a wannan hari kamar yadda jaridar yanar gizo Premium Times ta ruwaito.
“Maharan sun far wa kasuwar ne a daidai lokacin da jama’a ke tsaka da hada-hadar kasuwanci, kawai sai wadannan mutane suka fado cikin kasuwar suna harbin kan mai uwa da wabi. Nan take wasu ‘yan kasuwa uku suka rasa rayukansu sannan wasu har bakwai sun samu raunuka.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar hakan, inda ta kara da cewa tuni jami’ai suka fantsama domin kamo wadannan ‘yan taratsi.
Idan ba a manta ba a daren Juma’ar makon da ya gabata ne wasu mahara suka far wa wani Kauyen Fulani a Taraba inda suka kashe shanu har 150.
Shi ma wannan harin ya auku ne cikin dare kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa rundunarsa ta maida hankali don ganin an kamo masu aikata irin wadannan munanan ayyuka a fadin jihar.