’Yan bindiga sun kai hari kasuwar Taraba, sun yi awon gaba da mutum 3

’Yan bindigar dai sun yi awon gaba da dilolin hatsi guda uku.

’Yan bindiga sun kai hari kasuwar Taraba, sun yi awon gaba da mutum 3

Wasu ’yan bindiga a Najeriya.

Wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun kutsa kasuwar hatsi ta garin Pakri da ke Karamar Hukumar Bali ta Jihar Taraba, sannan suka yi awon gaba da wasu dilolin hatsi su uku.

Aminiya ta gano cewa maharan, wadanda yawansu ya kai kusan 12, sun yi wa kasuwar kawanya ne wacce ke kan hanyar Jalingo zuwa Bali da sanyin safiyar Lahadi, sannan suka sace ’yan kasuwar.

Harin dai ya tilasta dakatar da hada-hadar a kasuwar, inda mutane suka rika guduwa suna barin kadarorinsu zuwa kan tsaunuka da dazuka don tsira da rayukansu.

Lamarin dai na zuwa ne kwana biyu bayan masu garkuwa sun sace wani tsohon ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya da wasu mutum uku a Anguwar Baraya da ke birnin Jalingo.

A ’yan makonnin nan, kauyukan Jihar Taraba dai sun sha fama da hare-haren ’yan bindiga, inda aka sace kusan mutum 30, ciki har da Hakimin Amar.

Yankunan da aka kai wa harin dai sun hada da Karim-Lamido da Bali da Jalingo da kuma Gassol.

Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da kai harin, amma ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani daga baturen ’yan sanda (DPO) na yankin ba.