‘Yan bindiga sun kai hari kauyukan Katsina sun kashe mutum 10
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan `Yar Santa da Sherere a karamar hukumar Kankara sun kashe mutum 10 tare da jikkata wasu da dama. Mazauna kauyen sun ce, ‘yan bindigar sun afkawa garin ne a babura inda suka fara harbin jama’a tare da kone gidaje da motocin jama’ar kauyukan. Wani shugaba a unguwar mai […]
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan `Yar Santa da Sherere a karamar hukumar Kankara sun kashe mutum 10 tare da jikkata wasu da dama.
Mazauna kauyen sun ce, ‘yan bindigar sun afkawa garin ne a babura inda suka fara harbin jama’a tare da kone gidaje da motocin jama’ar kauyukan.
Wani shugaba a unguwar mai suna Dikko Sherere, ya bayyanawa wakilinmu ta wayar sadarwa cewa, a yanzu haka suna fargabar fita yi wa wadanda aka kashe jana’iza saboda harin ‘yan bindiga.
Cikakken rahoton na nan tafe.