’Yan bindiga sun kai wa mahaifiyar Gwamnan Taraba hari
Wasu da ake zargi ’yan bindiga ne sun kai wa mahaifiyar Gwamnan Jihar Taraba, Jumai Kefas da ƙanwarsa, Atsi Kefas, hari. Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne jiya Juma’a a hanyar Wukari zuwa Kente da ke Ƙaramar Hukumar Wukari ta jihar. Mutum biyu sun shiga hannu kan safarar makamai a hanyar Zariya Dubun […]
Wasu da ake zargi ’yan bindiga ne sun kai wa mahaifiyar Gwamnan Jihar Taraba, Jumai Kefas da ƙanwarsa, Atsi Kefas, hari.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne jiya Juma’a a hanyar Wukari zuwa Kente da ke Ƙaramar Hukumar Wukari ta jihar.
- Mutum biyu sun shiga hannu kan safarar makamai a hanyar Zariya
- Dubun mai damfarar masu cirar kudi a ATM ta cika
Da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, Shugaban Ƙaramar Hukumar Wukari ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa wasu mutane da ke kan babura ne suka yi yunƙurin tsayar da motar da ta ɗauko mahaifiyar gwamnan da ’yar uwarsa, inda jami’an ’yan sandan da ke tare da su suka yi harbe-harbe a iska a yayin faruwar lamarin.
Kazalika, bayanai sun ce ’yar uwar gwamnan — Atsi Kefas— ta ji raunina harsashin bindiga, inda likitoci a Asibitin Koyarwa na Wukari suka duba lafiyarta gabanin garzaya wa da ita Abuja domin samun ƙarin kulawar mahukuntan lafiya.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Taraba, SP Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin ba tare ƙarin haske ba.
Sai dai ya bayyana cewa, lamarin ya rutsa ne da wata mota da ta fito daga gidan gwamnan kuma mutum ɗaya a ciki ya ji rauni.
Ƙoƙarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin mai magana da yawun Gwamnan Taraba, Mista Emmanuel Bello ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.