’Yan bindiga sun kai wa masallata hari a Birnin Gwari

Mazauna ƙauyen sun tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkatar wasu sakamakon harin.

’Yan bindiga sun kai wa masallata hari a Birnin Gwari

Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan gomman Musulmai a yayin da suke sallar Juma’a a wani yanki na Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

’Yan bindigar sun kai hari ne a Unguwar Makera da ke yankin Kwasakwasa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a lokacin da Musulmai ke sallar Juma’a da misalin ƙarfe biyu na rana.

Mazauna ƙauyen da shugabannin al’ummar yankin sun tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkatar wasu sakamakon harin.

Wani shugabann al’ummar ƙauyen, Malam Muhammad Hudu ya ce ’yan bindigar sun buɗe wuta kan masallatan lamarin da ya tilasta musu tsere a daidai lokacin da suke raka’ar ƙarshe.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kaduna Mansur Hassan ya tabbatar da kai harin ko da yake bai yi ƙarin bayani kan mutanen da suka mutu ko jikkata ba.

Harin na ranar Juma’a na faruwa ne kwanaki kaɗan bayan ’yan bindiga sun sace ɗalibai sama da 280 da malamansu a wata makarantar firamare ta ƙauyen Kuriga da ke Karamar Hukumar Chukun a jihar ta Kaduna.

Ɗan bindiga ya harbe alƙalai 2 a harabar Kotun Ƙolin Iran

’Yan Yahoo sun harbe jami’in EFCC har lahira a bakin aikinsa

Farashin kayan abinci ya faɗi warwas a Neja

Gaza: Yadda za a yi musayar fursunonin Palasdinawa da Isra’ila