’Yan bindiga sun kama ‘barawo’ a Katsina, sun mika shi ga hukuma

Sun ce ya kamata a tabbatar an hukunta shi bisa doka

’Yan bindiga sun kama ‘barawo’ a Katsina, sun mika shi ga hukuma

Masu Garkuwa da Mutane

A wani yanayi mai cike da daure kai, ’yan bindiga a jihar Katsina sun kama wani dan jari-bola da suka kama yana sace-sace a kauyen da mutanen garin suka gudu suka bari.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa wanda ake zargin, wanda matashi ne ya kware wajen cire rodika da karafa daga ginin mutane a wani kauye.

Kafar ta rawaito cewa ’yan bindigar sun kama matashin ne lokacin da suka fito sintiri a kan baburansu.

A wani bidiyo da kafar ta samu, an ga ’yan bindigar suna gabatar da shi tare da karafan da ya sata a gaban wani shugaban al’umma na kauyen.

Sai dai kafar ba ta iya tantance lokacin da aka nadi bidiyon ba.

“Ba ka san sata laifi ba ce? Ka yi sa’a za mu mika ka ga hukuma, da kashe ka za mu yi,” inji ’yan bindigar.

’Yan ta’addan dai, wadanda aka gani a bidiyon rike da muggan makamai, sun gargadi shugaban da ya tabbatar an hukunta barawon daidai da doka don ya zama izina ga masu hali irin nasa.

Kazalika, majiyar ta ce ba wai kawai damka matashin suka yi ga hukuma ba, sun kuma tabbatar da cewa daga bisani jami’an tsaro sun yi awon gaba da shi don a titsiye shi.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo