’Yan Bindiga Sun Karbe Wuraren Hakar Ma’adanai A Zamfara

‘Yan jarida ba sa fadin kusan kashi 60 cikin 100 na matsalar tsaron da ake fuskanta a Zamfara.

’Yan Bindiga Sun Karbe Wuraren Hakar Ma’adanai A Zamfara

Harkar tsaro a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da tabarbarewa duk da kokarin da Gwamnatin jihar da ta Tarayya ke cewa na yi wurin yaki da ta’addanci.

Wani mazaunin Karamar Hukumar Anka ta jihar wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana lamarin a matsayin wanda ya gagari kundila.

A cewarsa, matsalar ta kai ga ‘yan bindiga sun mamaye yankunan da ake hakar ma’adinai a cikin karamar hukumar, inda al’ummar yankin suka zabi yi wa ‘yan taadan aiki kan kudaden da ba su taka kara sun karya ba.

Mazauna wannan yanki, sun bayyana mana cewa suna rayuwa cikin halin rashin tabbas, sun manta lokacin da suka kwana a cikin gidajensu da ido rufe.

A koda yaushe suna rayuwa cikin barazanar hare-hare, lamarin da ke tilasta musu neman mafaka a cikin dazuka, inda wasu ke kwana a kan bishiya.

Karar harbe-harben bindiga da ‘yan ta’adda ke harbawa wani lamari ne mai ban tsoro ga rayuwar al’ummar yankin Anka.

Karamar Hukumar Anka, wacce a da take daya daga cikin wuraren da ake zaman lafiya, a yanzu ta shiga cikin matsalar rashin tsaro, inda ake ganin a ko yaushe za a iya samun harin ‘yan ta’adda.

Lamarin dai ya kai wani matsayi mai ban tsoro, ta yadda hatta taimakon kai da al’umma ke yi na Kato da Gora (Baga) ya zamo tarihi, saboda ‘yan taadan sun yi karfi na ban mamaki.

Abdulmutallib Ja’afar, malami a Jami’ar Jihar Zamfara da ke Mafara, kuma ma’aikacin agaji, ya ce abin da ‘yan jarida ke bayyanawa kamar kaso arba’in ne, ba a fadin kusan kashi 60 cikin 100 na matsalar tsaron.

Ya bayyana cewa Jihar Zamfara, ciki har da babban birnin jihar wato Gusau, a yanzu ya zama wani wuri mai hatsarin gaske, wanda babu wanda ke da kwanciyar hankali.

Yin garkuwa da mutane, ko kashe su, ko a raunata su, ko a wawashe kayan su, lamari ne da ya zama ruwan dare.

Wani masanin tsaro kuma mai sharhi akan harkokin tsaron a Najeriya, Detective Auwal Durumin Iya ya danganta tabarbarewar tsaro a Zamfara da rashin hadin kai da ke tsakanin gwamnatin jihar da na Tarayya a wurin yaki da ‘yan ta’adan.

Mun tuntubi Babban Sakataren Yada Labarai na  Fadar Gwamnan Zamfara, Jafaru Kaura, wanda ya ce mu tuntubi Ambasada Bala Mairiga, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar a matsayin wanda ke da alhakin amsa tambayoyi.

Sai dai duk kokarin jin ta bakin Ambasada Bala ya ci tura, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS