’Yan bindiga sun karbi sigari a cikin kudin fansar mutum takwas
Sun yi garkuwan da mutanen da ke taron makokin dan uwansu.
’Yan bindiga sun karbi kwalin taba sigari da madara a matsayin fansar wasu mutum takwas da suka yi garkuwa da su a wurin jana’iza.
’Yan bindigar sun yi awon gaba da mutanen ne a kauyen Itapaji da ke Karamar Hukumar Ikole a Jihar Ekiti, lokacin da mutanen suke shirin gudanar da bikin jana’izar wani dan uwansu da ya rasu.
Yi wa gidan mutanen dirar mikiya ne da misalin karfe 9:30 na dare, suka shafe kusan awa guda suna harbe-harbe, daga bisani suka kwashe mutanen gidan gaba daya.
Bayan sako mutanen, sun bayyana cewa sai da suka bai wa masu garkuwa da su Naira miliyan biyu da dubu dari biyar da kwalin taba sigari da na madara sannan suka sako su a ranar Alhamis.
Mai magana da yawun ’yan sanda na jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu ne tabbatar da faruwar al’amarin lokacin bayan masu garkuwa da mutanen sun sako mutanen gaba daya.
Ya ba da tabbaci cewa za a ci gaba da gudanar da bincike kan wasu mutum hudu da ake zargin suna da da hannu a garkuwa da mutanen da aka yi.