’Yan bindiga sun kashe ƙaramar yarinya da wasu mutum 2 a Kaduna
Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance game da harin
Wata yarinya ’yar shekara bakwai da wasu mutum biyu sun rasu sakamakon harin da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Kuki da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
Maharan sun kai harin ne a ranar Litinin da rana.
- ’Yan sanda sun kama mutum 721, sun ƙwato motoci 13 a 2024 a Borno
- Harin Silame: Masana sun gargaɗi sojoji kan rashin sanar da gwamnoni
Wasu mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun zo a kan babura, inda suka sace dabbobi, sannan suka kai farmaki kasuwannin ƙauyen, wanda ke kan iyakar Jihar Kaduna da Jihar Neja.
Shugaban wata al’umma, wanda bai so a bayyana sunansa, ya ce an samu gawar yarinyar a cikin daji bayan kai harin.
“’Yan bindigar sun shigo ta ƙauyen Unguwar Mission, sun sace awaki, babura, sannan suka kai wa kasuwanni hari.
“Mutane biyu sun mutu, kuma an samu gawar yarinyar a cikin daji,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, wasu mutane daga Neja da Randagi sun dawo da awakin da aka sace.
Shugaban Ƙungiyar Birnin Gwari-Niger Inter Boundaries Communities Union for Peace and Development, Ishaq Usman Kasai, ya tabbatar da harin amma ya ƙi yin ƙarin bayani.
Babu wata sanarwa daga gwamnati ko ’yan sanda game da harin.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya ci tura domin ba ya ɗaga waya.