’Yan bindiga sun kashe basarake a Kwara
Maharan sun sace matar basaraken tare da wa su mutum biyu.
’Yan Bindiga sun kai hari Fadar Olukoro da ke yankin Koro a Karamar Hukumar Ekiti a Jihar Kwara, inda suka kashe basaraken yankin, Janar Segun Aremu (mai ritaya).
’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da matar sarkin da wasu mutum biyu.
- Shin Da Gaske Ýan Jarida A Najeriya Na Zuzuta Matsalar Tsaron Kasar?
- Za a buɗe makarantu 23 da aka rufe tsawon shekaru 10 a Oyo
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar da safiyar ranar Juma’a.
A cewarta, “Ana ci gaba da gudanar da bincike don kama wadanda suka aikata laifin.
“Muna tabbatar wa jama’a cewa, ba za a kyale wadanda suka aikata wannan laifi ba tare da an gurfanar da su ba.
“An tsaurara matakan tsaro a yankin Koro, don tabbatar da tsaro da jin dadin mazauna yankin”.
Ta ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Victor Olaiya, “Ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, domin rundunar na aiki tukuru don cafke masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.”
Gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana kisan basaraken a matsayin “abin tashin hankali, abin tsoro, kuma abin Allah-wadai”.
AbdulRazaq, ya kuma bukaci jami’an tsaro da kada su yi kasa a gwiwa wajen gano ‘yan bindigar da suka kashe basaraken.
“Tabbas za mu gano wadanda suka aikata laifin kuma za mu tabbatar da cewa wannan shi ne laifinsu na karshe da za su aikata.
“Ina mika ta’aziyyata ga al’ummar Koro. Muna cike da bakin ciki,” cewar gwamnan.