’Yan bindiga sun kashe direba, sun kwashe fasinjoji a hanyar Jibiya da rana tsaka

Sun kashe direban motar sannan suka kwashe fasinjoji

’Yan bindiga sun kashe direba, sun kwashe fasinjoji a hanyar Jibiya da rana tsaka

‘Yan Bindiga

’Yan bindiga sun tare hanyar Jibiya da ke Jihar Katsina, inda suka bude wa motar Hukumar Sufuri ta Jihar (KSTA) wuta da ke makare da fasinjoji.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da wajen misalin karfe 12:00 na ranar Lahadi.

An tare hanyar ne a tsakanin kauyen Mil Takwas da garin Farun Bala.

Maharan sun kashe direban motar suka kuma kwashi fasinjoji bayan jikkata wasu da suka yi.

Harin na zuwa ne a ranar da kasuwar garin na Jibiya ke ci, a kan hanyar da take da shingen bincike fiye da ashirin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Katsina ba ta ce komai ba a kan harin.

Venezuela na ci gaba da samun tallafi bayan mummunar girgizar ƙasa

PRP ta yi fatali da shirin kafa ’yan sandan jihohi

Sojoji sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa a Zamfara

An umarci bankuna su rufe asusun masu alaƙa da ta’addanci