’Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 40 a jihohin Benuwai da Nasarawa

Wadanda suka mutu a harin da ’yan bindiga suka kai kauyen Akukoro da ke karamar Hukumar Guma da ke Jihar Benuwai ya haura 30, bayan da ’yan bindigar da ba a san ko su wane ne ba suka sake kai hari da safiyar Lahadin da ta gabata.Hare-hare a kauyukan karamar hukumar sun shafi kauyukan Iyordye […]

’Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 40 a jihohin Benuwai da Nasarawa

‘Yan gudun hijirar da rikicin kan iyakar Jihar Nasarawa da Benuwai ya raba da muhallinsu da ke garin Adudu. Wadanda suka mutu a harin da ’yan bindiga suka kai kauyen Akukoro da ke karamar Hukumar Guma da ke Jihar Benuwai ya haura 30, bayan da ’yan bindigar da ba a san ko su wane ne ba suka sake kai hari da safiyar Lahadin da ta gabata.
Hare-hare a kauyukan karamar hukumar sun shafi kauyukan Iyordye da Akaahena da Nzorob inda ake zargin ’yan bindigar cikin kakin soja sun kashe mutum 20 tare da kone gidaje da dama a hari na bayan nan.
Wata majiya ta ce, “Sun fito ne daga Jihar Nasarawa da ke makwabtaka da wurin, da safiyar Lahadi, kuma suna da yawa dauke da miyagun makamai inda suka mamayi kauyen Akuroko suna harbe-harbe da kone duk ginin da suka ci karo da shi.”
Wani mazaunin kauyen ya ce, “Ba zan iya cewa ga adadin mutanen da aka kashe ba, har sai mun san halin da sauran mutanenmu suke ciki, amma a yanzu zan iya cewa an kashe kimanin mutumn 34 a wannan hari, kuma da dama sun samu raunuka.
Shugaban karamar hukumar, Francis Adii, wanda ya tabbatar da aukuwar rikicin, ya ce maharan sun mamayi kauyen Akuroko da safiyar Lahadi, inda suka rika kisa da kone gidaje da bukkokin da ke kauyen.
Ya tabbatar da mutuwar mutum 10, yayin da wasu suka samu raunuka, kuma a cewarsa a yanzu haka suna jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benuwai.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Daniel Ezeala ya ce har zuwa lokacin rundunar ba ta samu bayani kan lamarin ba.
Daga Jihar Nasarawa kuma wakilinmu a ruwaio cewa akalla mutum 10 ne ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kashe a kauyen Jangargari da ke karamar Hukumar Awe a kan iyakar jihar da Jihar Binuwai a karshen makon jiya.
Aminiya ya gano cewa ’yan bindigar da suka yi wannan aika-aikar wadanda suka fara kai hari a kauyen Lordye a Jihar Binuwai ne, inda daga wajen ne suka shigo kauyen Jangargari suka kashe mutanen suka kuma kone gidaje da motoci da dama.
A halin yanzu dai wadanda suka bar gidajensu sakamakon harin suna gudun hijira ne a wadansu kauyuka da ke kewaye da su.
A ganawar da wakilinmu ya yi da shi game da lamarin, shugaban matasan kabilar Tibi a Jihar Nasarawa Mista Peter Igbache ya zargi Fulani da kai harin inda suka kashe ’yan kabilar Tibi. Ya ce, “Fulani sun shigo yankinmu da manyan makamai inda suka kashe mutanenmu suka kuma kone mana gidaje da motoci. Sun kashe wani Mataimakin Kwamishinan ’yan sanda da ’yan uwansa uku a harin da Fulani suka kai kauyen. A gaskiya ba ma jin dadin halayen da jami’an tsaro a jihar nan ke nunawa a duk lokacin da abu irin wannan ya auku.”
Sakataren kungiyar Miyyati Allah Kataul Hore na jihar Malam Muhammad Hussain ya ce, “Wadannan mayakan Tibi ne sun fito ne daga Jihar Binuwai inda suka kai hari ga Fulani suka kuma rikitar da shanu da dama wadanda a halin yanzu sun bace a daji. Sun kai hari ne a kauyen Jangargari suka kashe wadansu da dama wadansu kuma suna gudun hijira a garurruwan da ke makwabtaka da su, kamar Adudu da Awe da Obi da sauransu. Amma abin bakin ciki har yanzu rundunar ’yan sandan jihar nan ba ta dauki wani mataki game da haka ba.”
Wakilinmu ya ziyarci garin Adudu, inda ’yan gudun hijirar da lamarin ya shafa suke zaune, kakakinsu wani dattijo mai suna Malam Salihu Aliyu, ya ce, “Lamarin ya auku ne da safe ranar Asabar inda aka wayigari wadansu ’yan bindiga wadanda daga baya muka samu labarin cewa su ne suka kai hari a wani kauye a Jihar Benuwai suka kashe mutane. Su ne suka shigo kauyenmu suka kashe mana mutane da kona motoci da kuma gidaje. Ina kira ga rundunar ’yan sandan jihar nan da sauran jami’an tsaro su turo jami’an tsaro yankin namu don ba mu damar komawa gidajenmu mu cigaba da harkokinmu na yau da kullum. Kuma a tabbatar an kamo wadanda suka aikata wannan bala’i a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.”
Wata ’yar kabilar Tibi, Misis Polina Ahende ta ce, “A gaskiya mun yi asarar rayukan ’yan uwanmu da dukiyoyinmu sosai sakamakon harin da ’yan bindigar suka kai mana ba zato babu tsammani a Jangargare a karshen mako. Sun kashe mana maza da yara kanana. Ba mu san ko wadanne irin mutane ne ba. Saboda haka nake kira ga gwamnati da sauran al’umma mawadata su taimaka mana da abin da za mu ci mu ba wa yaranmu a nan. Gwamnati da jami’an tsaro su kawo karshen tashin-tashinar da ke yawan addabar yankinmu a ’yan kwanakin nan.”
 A hedkwatar Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa kakakinta Mista Cornelius Ocholi ya ce rundunar ba ta samu labarin harin da aka kai yankin ba tukun. Ya ce akwai jami’an tsaro da dama da rundunar ta kafa a yankunan karamar Hukumar Awe da sauran kananan hukumomin jihar a kokarinsu na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Ya gargadi al’ummar jihar su daina daukar doka a hannunsu maimakon haka su rika kai kara wurin hukumomi da suka dace a duk sa’adda wata matsala ta taso..
Ya ce ’yan sanda da sauran jami’an tsaro a shirye suke su hukunta duk wanda aka kama yana kawo tashin hankali a jihar, musamman a wannan lokaci da jihar ke fuskantar matsalolin tsaro.
Saudayawa dai a duk lokacin da ’yan bindiga suka kai hari a yankin kudancin jihar da kabilun Fulani da Tibi suka fi yawa, za a ga suna zargin junansu.