’Yan bindiga sun kashe Hakimi a Kudancin Kaduna

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe Hakimin Zangang da ke masarautar Atakar a karamar Hukumar kaura a Jihar Kaduna, Mista Yohanna Daniel Shinkut. Wani mazaunin yankin Emmanuel Samuel ya ce ’yan bindigar sun kashe Hakimin ne a kan hanyarsa ta komawa gida daga garin Manchock. “Al’amarin ya […]

’Yan bindiga sun kashe Hakimi a Kudancin Kaduna
’Yan bindiga sun kashe Hakimi a Kudancin Kaduna

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe Hakimin Zangang da ke masarautar Atakar a karamar Hukumar kaura a Jihar Kaduna, Mista Yohanna Daniel Shinkut.

Wani mazaunin yankin Emmanuel Samuel ya ce ’yan bindigar sun kashe Hakimin ne a kan hanyarsa ta komawa gida daga garin Manchock. “Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare a ranar Juma’a lokacin da maharar suka bude wa motarsa wuta da bindigogi. Motar ta yi matukar lalacewa, bayan ta tsaya sai ne suka karasa kusa da shi suka harbe shi a kirji,” inji shi.
daya daga cikin dattawan yankin mai suna Enoch Zangang ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana abin da ya faru da abin bakin ciki. Enoch ya ce an yi wa basaraken mummunan kisa ne a kan hanyarsa ta komawa gida. Ya ce gawarsa na ajiye a asibitin Manchok.
“Abin da ke faruwa a yankinmu tun a watan Afrilun shekarar 2013, yaki ne da wasu ke yi da jama’armu da nufin kawar da da jinsinmu daga doron kasa. Abin damuwa ne kwarai da gaske. Mutane ake ta kashewa kuma babu mai kawo musu dauki. Akalla mutane kusan 600 aka kashe a masarautarmu. Dole ne a dauki mataki a kan hakan,” inji shi.
Gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa ta ofishin Kakakin Gwamnan, Malam Ahmed Maiyaki inda ya ba jama’ar yankin hakuri kan abin da ya faru. “Gwamnati ba za ta amince da wadannan kashe-kashe da ake yi a yankin ba. Kuma a shirye muke mu dauki matakan da suka dace domin kare al’umnarmu,” inji shi.
Gwamnatin ta kuma roki jama’ar jihar su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da juna.

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 sun sace dabbobi a Bakori