’Yan bindiga sun kashe Hakimin da suka sace a Bauchi

An yi jana’izarsa a ranar Lahadi bayan, an tsinci gawarsa a gefen hanya.

’Yan bindiga sun kashe Hakimin da suka sace a Bauchi

’Yan bindiga sun kashe Hakimin Kauyen Riruwai da ke Gundumar Lame a masarautar Bauchi a Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Garba Badamasi.

Aminiya ta ruwaito cewa tun da farko wasu ‘yan bindiga ne da suka kai hari tare da yin garkuwa da shi a ranar Juma’a, 15 ga watan Maris, 2024.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce ‘yan bindigar sun shiga fadar marigayin kai tsaye, inda suka yi awon gaba da shi.

Majiyar ta ce marigayin ya shafe kwana daya a hannun ’yan bindigar kafin daga bisani suka kashe shi tare da jefar da gawarsa a kan hanyar kauyen.

Bayan tsintar gawar tasa a ranar Lahadi, an yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Daya daga cikin masu sarautar gargajiya na kauyen ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, ta ci tura domin bai amsa kiran da aka masa ba.

Don namen mulki ’yan siyasa ke sukan Tinubu —Gwamnan Kaduna

Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani

Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji

Kotu ta tsige Ohinoyi na Ƙasar Ebira