‘Yan bindiga sun kashe Hakimin Soro
Wasu ’yan bindiga su shida sun kashe Hakimin Soro da ke karamar Hukumar Ganjuwa Jihar Bauchi da wasu mutum biyu suka kuma raunata mutum guda.Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Haruna Mohammed ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, inda ya ce ’yan bindigar da […]
Wasu ’yan bindiga su shida sun kashe Hakimin Soro da ke karamar Hukumar Ganjuwa Jihar Bauchi da wasu mutum biyu suka kuma raunata mutum guda.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Haruna Mohammed ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, inda ya ce ’yan bindigar da aka zaton ’yan fashi ne sun suka kashe hakimin Alhaji Abdurrahman Isa Baba mai shekara 45 da mutanen kafin su sace makudan kudi su gudu.
Ya ce a yanzu haka ’yan sanda sun kewaye yankin a kokarinsu na kamo wadanda suka aikata laifin kuma ya roki al’umma su ci gaba da ba ’yan sanda bayana da za su taimaka wajen kama masu laifin.
Wani mazaunin garin ya shaida wa manema labarai cewa sun ji karar bindigogi a garin Soro lokacin da ’yan bindigar suka shigo hakan ya sa kowa ya tsere gida ya buye.
Ya ce bayan da kura ta lafa ne aka tarar ’yan bindigar sun kashe wani dan kasuwa a shagonsa kuma da aka je gidan Hakimin aka tarar sun harbe shi tare da wani kanensa mai suna Ahmadu.
DSP Haruna Mohammed ya ce rundunarsu ta kame bindigogi tare da gano sinadaran hada bam da harsasai da aka kunshe a bututun abin kashe gobara da aka bisne a cikin wani gida a garin Azare hedkwatar karamar Hukumar Katagum da ke jihar.
DSP Haruna ya ce masu bincike na rundunar sun kama wani mai suna Yahaya Adamu Abubakar mai shekara 32 da ke zaune a Unguwar kofar Dumi kan lamarin.