’Yan bindiga sun kashe jami’an FRSC uku a Kebbi
An kashe sama da jami’an kwastam, da na shige da fice da ’yan sanda 10 a yankin Tsamiya/Maje a irin waɗannan hare-hare.
A wani hari da aka kai a ƙarshen makon nan, ’yan bindiga sun kashe jami’an Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) guda uku a kan hanyar Tsamiya–Illo da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo a Jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce jami’an da abin ya shafa sun haɗa da DCRMA Umar Aliyu, SRMA Ezra Manu Gona da RMA I Mansur Ibrahim Nasir.
- An ci gaba da luguden wuta yayin da yaƙin Iran da Amurka ya cika kwanaki 100
- ADC na neman Gawuna ya tsaya mata takarar Gwamnan Kano
Wata majiya daga yankin ta ce jami’an na kan aikin su ne lokacin da ’yan bindigar suka kai musu harin na kwanton ɓauna.
A cewar majiyar, jami’an sun yi yunƙurin tserewa, amma ’yan bindigar da ke kan babura suka bi su har suka riske su suka kashe su kafin su samu damar shiga daji domin tsira.
Majiyar ta ƙara da cewa maharan, waɗanda aka ce sun haura 20, sun koma cikin daji nan take bayan wannan mummunan hari.
Ta ce yankin Tsamiya ya daɗe yana fuskantar hare-haren ’yan bindiga da kuma mayaƙan Lakurawa, inda aka sha kai farmaki kan jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati a baya.
Rahotanni sun nuna cewa tun daga bara zuwa yanzu, an kashe sama da jami’an kwastam, da na shige da fice da ’yan sanda 10 a yankin Tsamiya/Maje a irin waɗannan hare-hare.
Har zuwa yanzu dai, hukumar FRSC ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kira taron gaggawa domin duba yadda za a ƙarfafa matakan kare jama’a da jami’an gwamnati.
Ya kuma bayyana damuwa kan yawaitar hare-hare, tare da jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci masu taimaka wa ’yan bindiga ba, yana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsauri.