’Yan bindiga sun kashe jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice biyu a Sakkwato

Ana fargabar cewa matsalar tsaro ta sake dawowa a Jihar Sakkwato.

’Yan bindiga sun kashe jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice biyu a Sakkwato

Sakkwato

’Yan bindiga sun kai farmaki a wani shingen bincike na jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya da ke Karamar Hukumar Gwadabawa a Jihar Sakkwato.

Majiyar rahoton ta ce maharan wadanda suka bude wa jami’an wuta, sun harbe jami’ai biyu nan take yayin da aka garzaya da wasu hudu zuwa asibiti.

Wani direba da ya ba da shaidar faruwar lamarin a kauyen Mammansuka, ya ce maharan haye a kan babura sun bude wa jami’an wuta ne bayan sallar Magriba a ranar Juma’ar da ta gabata.

Mammansuka tana cikin manyan kasuwannin da ke ci duk mako wadda ke kan hanyar Sakkwato zuwa Illela har Kasar Nijar.

Majiyar ta ce ba a san dalilin da ya sa aka kai harin ba la’akari da cewa jami’an ba su takurawa mutanen gari sai dai baki da ba su da takardun izinin shigowa Najeriya.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar a yankin Illela, Bello Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai a lokacin da aka kira shi yana asibiti ya ce zai kira daga baya.

Da wakilimu ya sake kiran shi bai samu wayarsa ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Ana fargabar cewa matsalar tsaro ta sake dawowa a Jihar Sakkwato, yayin da kusan kullum sai an kai wa al’umma hari ina ake  kashewa ko sacewa ko jikkata wasu duk da kokarin da mahukunta ke fadin suna yi a harkar tsaron jiha.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja