’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo
An kai harin na kwanton ɓauna ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Juma’a, 5 ga Agusta, 2025.
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun hallaka jami’ai takwas na Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) da ke aiki a kamfanin siminti na BUA da ke Okpella, karamar hukumar Etsako East ta Jihar Edo.
An kai harin na kwanton ɓauna ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Juma’a, 5 ga Agusta, 2025, lokacin da jami’an suka fita raka wasu ma’aikatan kamfanin ’yan ƙasar China guda biyar bayan kammala aikin gadi a ƙofar kamfanin.
Wani babban jami’in rundunar a jihar ne ya bayyana haka a ranar Asabar, inda ya ce ’yan bindigar sun kuma jikkata jami’ai huɗu waɗanda ke karɓar magani a asibiti a halin yanzu.
Majiyar ta ce maharan sun buɗe wuta kan jami’an ne inda suka kashe takwas daga cikinsu nan-take. Sun kama ɗaya daga cikin ‘yan China ɗin, yayin da aka kuɓutar da huɗu.
An bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi ba-ta-kashi da jami’an NSCDC inda suka yi ta musayar wuta kafin su tsere cikin daji da ɗan ƙasar Chinan.
Jami’in ya ce dakarun tsaro sun bazama neman wanda aka yi garkuwa da shi da kuma tabbatar da cewa an kama ‘yan bindigar.
Kwamandan rundunar NSCDC a Jihar, Gbenga Agun, ya kai ziyara inda lamarin ya auku da kuma jami’an rundunar da suka jikkata asibiti.