’Yan bindiga sun kashe kodinetan El-Rufa’i
Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun bindige kodinetan yakin neman zaben zababben Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i a kauyansu da ke karamar Hukumar Jama’a. Kakakin zababben Gwamnan, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Kaduna.Ya ce, ’yan […]
Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun bindige kodinetan yakin neman zaben zababben Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i a kauyansu da ke karamar Hukumar Jama’a.
Kakakin zababben Gwamnan, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Kaduna.
Ya ce, ’yan bindingar sun bi Mista Markus Ishaya ne har kauyansu na Atuku kasa a gundumar Atuku suka harbe shi.
Markus Ishaya ne kodinetan yakin neman zaben Nasir El-Rufa’i a gundumar Atuku kuma an ce ya taka rawa wajen nasarar da jam’iyyar ta samu a yankin.
“Iyalinsa sun sanar da mu cewa wasu ’yan bindiga ne suka dirar wa gidansa suka kuma bude masa wuta.’Yan bindigar su biyu rike da manyan bindigogi ba su dauki komai ba a gidan bayan kashe shi da suka yi. Kuma ’yan sandan yankin sun ziyarci gidan sun kuma tabbatar da aukuwar lamarin kuma tuni sun fara bincike a kai,” inji shi.
Aruwan ya kuma ce suna fata ’yan sanda za su binciko wadanda suka aikata wannan aika-aika domin a hukunta su.
Da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, Malam Nasir El-Rufa’i ya yi addu’a ga mamacin.
“Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Mista Markus Ishaya da kuma jama’ar wannan gari nasa a bisa halaka shi da aka yi. Kuma muna bai wa iyalinsa da abokan arziki hakurin wannan rashi da aka yi,” inji shi.