’Yan bindiga sun kashe Kwamandan ’Yan banga na Jihar Kaduna
Wadansu ’yan bindiga sun harbe Kwamandan ’Yan banga na Jihar Kaduna da sufeton ’yan sanda tare da sace ’ya’yan kwamandan ’yan bangar mata a Unguwar Katsinawa da ke Shika a karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna. ’Yan bindigar wadanda aka ce sun kai mutum 50, da suka kewaye unguwar da manyan bindigogi sun harbe Sufeto […]

Wadansu ’yan bindiga sun harbe Kwamandan ’Yan banga na Jihar Kaduna da sufeton ’yan sanda tare da sace ’ya’yan kwamandan ’yan bangar mata a Unguwar Katsinawa da ke Shika a karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
’Yan bindigar wadanda aka ce sun kai mutum 50, da suka kewaye unguwar da manyan bindigogi sun harbe Sufeto Abubakar Lolo da Kwamandan ’Yan bangar, Mustafa Gali, yayin da suka raunata Kofur Alhasan Magaji cikin dare ranar Asabar da ta gabata.
Mahaifin shugaban ’yan bangar, Malam Muhammadu Gali ya ce, da misalin karfe 1:00 na dare yana kwance sai dansa Mustafa ya kira shi ta waya cewa wadansu mutane sun kewaye gidansa suna ta dukan kofa, don haka yana neman a taimake shi. “Sai na tayar da yara muka kama hanya zuwa gidansa, mun bi ta makabarta sai muka ji harbe-harbe kuma aka biyo mu a guje ana harbi kamar ana yaki, garin gudu har na fadi, saboda harbi duk muka watse. Sai da gari ya yi kusan wayewa muka samu labarin sun harbe shi a ciki da hannu kuma an dauke shi zuwa asibitin Shika, inda daga baya ya cika,” inji shi.
Malam Muhammadu Gali ya ce, maharan sun tafi da ’ya’yan marigayin mata biyu wadanda suka isa aure.
Daga baya Aminiya ta samu labarin ’yan bindigar sun sako ’ya’yan marigayi kwamandan biyu da suka sace, sai dai babu wani bayani kan ko an biya kudin fansa ko a’a kafin a sako su.
Shugaban kungiyar ’Yan banga ta karamar Hukumar Giwa, Malam mai danjume Sule ya shaida wa wakilnmu cewa: “Mu jami’an tsaro na sa-kai saboda irin yadda muke gudanar da ayyukanmu mun yi bakin jini kwarai da gaske a wurin Fulani makiyaya da wadanda ba su son a yi gaskiya. Wadanda suka kawo hari wannan kauye namu yawansu zai kai 50 kuma dauke da manyan bindigogi, in ka ji yadda suke harbi kamar za su tada garin, ana ciki haka ne wadannan ’yan sanda suka kawo mana dauki, to su kuma ’yan bindigar babu inda ba su a jiye mutanensu dauke da manyan bindigogi ba, sai suka yi wa ’yan sandan kwanton-bauna suka bude musu wuta, su ma suka mayar da martani, suka harbi dan sanda daya a kai, suka harbi direbansu a hannu, shi kuma shugabanmu na ’yan sintiri suka harbe shi a ciki da hannu inda ya cika a asibiti, kuma sun sace ’ya’yansa ’yan mata biyu.”
Shugaban kungiyar ’Yan sintiri ta kasa, Alhaji Usman Muhammed Jahun ya ziyarci garin Giwa domin ta’aziyya da jajantawa, inda ya ce abubuwa suna faruwa kuma abubuwan sun yi tsamari amma da ’yan sanda suka taso abubuwan sun dan ragu. Ya ce duk da haka da sauran aiki musamman masu garkuwa da mutane da ’yan fashi. “Idan ka dauka daga Kaduna zuwa Birnin Gwari wadannan miyagun mutane har yanzu suna nan, akwai su a sauran wurare irin su Giwa, kuma rashin kula da mu da yadda aka bar mu kara-zube musamman a Jihar Kaduna suke jawo haka. Duk da cewa a harka irin ta tsaro ta bijilanti Jihar Kaduna ce kusan ta daya, amma shekara biyu da suka wuce gaskiya an samu matsala a harkar bijilanti an watsar da ita,” inji shi.
Ya ce mutanensu da yawa suna da ruwa-da-tsaki, wajen kokarin bayar da bayanan duk inda suka sani na maboyar batagari, sai ga shi su kansu yanzu tsaron kansu ya zamar musu matsala, in aka duba abin da ya faru da shugabansu na jihar.
Shugaban ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i a kokarin da yake yi wajen tabbatar da harkar tsaro a jiharsa ya rika zama da su a yi tsari mai kyau domin dawo da martabar aikinsu, inda ya ce wanda Gwamnan ya sa ya kula da harkar tsaro a jihar ya taba rusa duk wata kungiya da take gudanar da aikin tsaro a jihar, wanda hakan kuskure ne.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mukhtar Hussaini Aliyu ya ce samun labarin kai harin ne ya sa suka tura jam’ansu su kai dauki inda a lokacin suka yi musayar wuta da ’yan bidigar, wadda ta yi sanadiyyar rasuwar dan sanda daya da shugaban ’yan sintiti na Jihar Kaduna da raunata dan sanda daya da kuma da sace ’yan mata biyu. “Yanzu haka mun baza jami’an tsaro domin bincikowa da kamo wadanda suka yi wannan ta’asa,’ inji shi