’Yan bindiga sun kashe Lakcara, sun sace ’ya’yansa a Katsina
Maharan sun sace ‘ya’yansa biyu bayan sun kashe shi.
’Yan bindiga sun kashe wani malamin Jami’ar Tarayya Dutsinma (FUDMA) da ke Jihar Katsina, Dokta Tiri Gyan David.
Dakta David, shi ne Shugaban Sashen Harkar Noma na Jami’ar, a safiyar ranar Talata.
Wani mazaunin garin ya ce maharan sun sace biyu daga cikin ’ya’yan malamin bayan sun kashe shi.
Marigayin yana zaune ne a rukunin gidaje na Low-Cost da ke ƙaramar hukumar Dutsinma a Jihar Katsina.
Majiyar, ta ƙara da cewa ‘yan bindigar sun mamaye yankin da muggan makamai, inda suka riƙa harbe-harbe don tsorata mazauna yankin.
Kakakin rundunar ’yan sandan Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce rundunar za ta fitar da cikakken bayani game daga baya.
Idan ba a manta ba a baya-bayan nan ’yan bindiga sun sace wasu ɗaliban Jami’ar, wadanda ke zaune a wajen Jami’ar.
Daga baya maharan sun sako ɗaliban, amma hukumomin tsaro sun ce ba a biya kuɗin fansa ba.
Dutsinma dai na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar ‘yan fashin daji.
Amma an samu raguwar hare-hare a ’yan kwanakin nan, sakamakon ƙoƙarin da gwamnatin jihar da jami’an tsaro ke yi wajen magance matsalar tsaro.