‘Yan bindiga sun kashe likita da matarsa a Yola
Wasu ‘yan bindiga sun kashe likitan asibiti mai suna Mwajim Malgwi tare da matsarsa a wata gonar su da ke wajen garin Yola babban birnin jihar Adamawa. Malgwi, shi ne wanda ya mallaki asibitin Polyclinic a Yola, an samu rahoton kai masa hari ne a gonarsa da ke kauyen Boggare kusa da Ngurore a karamar […]
Wasu ‘yan bindiga sun kashe likitan asibiti mai suna Mwajim Malgwi tare da matsarsa a wata gonar su da ke wajen garin Yola babban birnin jihar Adamawa.
Malgwi, shi ne wanda ya mallaki asibitin Polyclinic a Yola, an samu rahoton kai masa hari ne a gonarsa da ke kauyen Boggare kusa da Ngurore a karamar Hukumar Yola ta Kudu, lamarin ya faru ne bayan tattaunawa da ma’aikatan gonar.
Kakakin Hukumar ’yan sandan jihar Othman Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce, a yanzu haka su na ci gaba da gudanar da bincike a yankin.