’Yan bindiga sun kashe Limami da wasu a Sakkwato

Lamarin ya yi sanadin mutuwar wasu mazauna ƙauyen guda biyu tare da tilasta wa ɗaruruwan mutane tserewa daga gidajensu.

’Yan bindiga sun kashe Limami da wasu a Sakkwato

An samu rahoton kashe Babban Limamin ƙauyen Talluje da ke Ƙaramar Hukumar Bodinga a Jihar Sakkwato ranar Laraba, bayan da ’yan bindiga suka kai hari a Talluje da maƙwabtanta ƙauyen Chofi.

Lamarin ya yi sanadin mutuwar wasu mazauna ƙauyen guda biyu tare da tilasta wa ɗaruruwan mutane tserewa daga gidajensu.

Harin, wanda ya fara da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, ya auka wa unguwanni biyu da ke Gundumar Danchadi, kuma ya shafe kusan sa’o’i biyu ana fafatawa.

Wannan lamari ya kawo adadin sanadin rasa rayukan Manyan limamai guda uku da rahotanni suka ce ’yan bindiga sun kashe a Jihar Sakkwato cikin ‘yan makonnin da suka gabata.

Majiyoyi daga yankin sun shaida wa wakilinmu cewa, maharan sun kai hare-hare na bai-ɗaya a lokaci guda a duka unguwanni biyu, inda suka riƙa harbi ba ƙaƙƙautawa kafin su tsere da adadin dabbobin da ba a tantance ba waɗanda suka sace.

“Hare-haren sun fara ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma kuma suka ci gaba har zuwa kusan ƙarfe 6:00 na yamma. ’Yan bindigar sun kashe Babban Limamin Talluje da wasu mutane biyu waɗanda har yanzu ba a tantance ko su wane ne ba,” in ji wani shugaban unguwa a Danchadi.

Ya ƙara da cewa, hare-haren sun haddasa gudun hijira, inda mazauna yankin, musamman mata da ƙananan yara, suka tsere da ƙafafunsu zuwa wurare mafi aminci a Danchadi da garin Bodinga.

“Yayin da nake magana da kai, mutane da yawa suna tserewa daga unguwanninsu ɗauke da kayayyakinsu bayan sun tsere daga asalin ƙauyukan da abin ya shafa,” in ji majiyar.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa, maharan sun kwashe dabbobi masu yawa, kodayake ba a iya tantance ainihin adadin su ba nan take.