’Yan bindiga sun kashe limami da wasu mutum 3 a Sakkwato
Mun kira jami’an tsaro domin su kawo mana ɗauki, har ma muka yi alƙawarin ba su kuɗin man fetur, amma ba su zo ba.
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani limami da wasu mutum uku tare da yin garkuwa da mazauna ƙauyen Illelar Dawagware 12 a Ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato.
Mazauna ƙauyen sun ce maharan waɗanda suke haye a kan aƙalla babura 9, sun kai harin ne da misalin ƙarfe 12:20 na daren Asabar wayewar gari Lahadi.
Bayanai sun ce maharan, waɗanda adadinsu ya kai kusan 30, sun shafe kusan minti 30 suna harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa.
- Rundunar Sojin Nijeriya ta yi wa manyan hafsoshinta sauye-sauyen muƙamai
- Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan sansanonin Sojin Amurka a Bahrain da Kuwait
Wani mutumin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mazauna ƙauyen sun yi ƙoƙarin daƙile harin, amma maharan sun fi ƙarfinsu.
A cewarsa, ’yan bindigar sun fara kutsa gidan limamin ƙauyen, inda suka kashe shi da wasu mutum uku, kafin daga bisani su riƙa shiga gidaje suna awon gaba da mutane 12.
’Yan bindigar sun kashe limaminmu, maƙwabcinsa da wani mutum guda. Daga bisani kuma suka yi garkuwa da mutum 12, waɗanda suka haɗa da mata takwas da maza huɗu,” in ji shi.
Majiyar ta kuma ce wani daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, Alhaji Samaila ya samu raunin harbin bindiga wanda ya karya masa hannu, inda a halin yana karɓar magani a wani asibiti da ke Sakkwato.
Mazauna ƙauyen sun kuma zargi jami’an tsaro da gaza amsa kiran neman ɗauki yayin harin.
“Mun kira jami’an tsaro da ke Goronyo domin su kawo mana ɗauki, har ma muka yi alƙawarin ba su kuɗin man fetur, amma ba su zo ba,” in ji majiyar.
Ya ce wannan shi ne hari na 24 da aka kai wa ƙauyen.
“Sun zo shekaru biyu da suka gabata suka kashe mutum bakwai ’yan gida ɗaya a cikin masallaci. Tun daga lokacin ba mu sake fuskantar wani hari ba sai yanzu.
“A ranar Lahadin da ta gabata ne ma wasu daga cikin mutanen da suka yi gudun hijira suka dawo ƙauyen bayan sun shafe kusan shekara biyu suna gudun hijira,” in ji shi.
Wani mazaunin ƙauyen da ya halarci jana’izar limamin ya ce tsoro ya mamaye al’ummar yankin, inda ya ƙara da cewa mazauna da dama sun yanke shawarar daina kwana a ƙauyen.
“Daga yanzu za su riƙa kwana a sansanin ’yan gudun hijira da ke Goronyo saboda suna tsoron sake afkuwar wani hari,” in ji shi.
Mazauna ƙauyen sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar, da kuma hukumomin tsaro, da su ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen hare-haren da ake ci gaba da kai wa yankin.
A ranar Larabar da ta gabata, Aminiya ta rawaito cewa wasu ’yan bindiga sun kashe wani babban limami tare da yin garkuwa da mutum tara a ƙauyen Kuda-Kuda da ke wannan yankin a Ƙaramar Hukumar Goronyo.