’Yan bindiga sun kashe ma’aikacin FIRS a Abuja
Maharan sun harbi matashin wanda ya fita sayen abinci a Unguwar Maitama da ke Abuja.
Wasu ’yan bindiga sun kashe wani matashi mai suna Khalid Ahmed Bichi a Unguwar Maitama da ke Abuja a ranar Juma’a.
Bichi, wanda aka ruwaito cewa ma’aikaci ne a Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS) ya yi gamo da ajalinsa ne da misalin ƙarfe 9 na dare a lokacin da ya fita sayen abinci.
- ’Yan Nijeriya za su ci moriyar sauye-sauyen haraji da muka kawo — Shettima
- Mai ’ya’ya 12 ya mutu a ɗakin karuwarsa
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa maharan sun harbi matashi sau dama kafin su ranta a na kare.
Bayanai sun ce bayan faruwar lamarin, an garzaya da matashin Babban Asibitin Maitama, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Tuni dai an binne mamacin bayan jana’izarsa da aka gudanar da ƙarfe 1:30 na ranar Asabar a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin wanda ya shahara da sunan @KhalidBichi musamman a shafin X (Twitter) yana da alaƙa da manyan ’yan siyasa a ƙasar.
Dare Adekanmbi, mai ba da shawara na musamman kan harkokin sadarwa ga Shugaban hukumar ta FIRS, Zacch Adedeji, ya ce ba su da wani cikakken bayani a kan lamarin da a yanzu haka yana hannun hukumar ’yan sanda.
Sai dai ya ce hukumar tana cikin jimamin rashin ɗaya daga cikin ma’aikata yayin da kuma take miƙa saƙon ta’aziyya zuwa ga mata da kuma ’yan uwan mamacin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta ce sun ƙaddamar da bincike a kan lamarin.
Cikin wata sanarwar da SP Josephine Adeh ta fitar ta ce Kwamishinan ’yan sandan Abuja ya bayar da uamrnin gaggauta gudanar da bincike domin gano waɗanda suka kashe matashin
Sanarwar ’yan sanda ta ambato kwamishinan na tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta yi duk abin da ya kamata domin kamo waɗanda ake zargi da kisan matashin domin gurfarar da su agaban shari’a.
Kisan matashin dai ya ja hankalin al’umma, musamman a shafukan sada zumunta, inda mutane suka yi ta nuna alhininsu da bayyana kaɗuwarsu kan lamarin.