’Yan bindiga sun kashe ma’aikatan kamfanin manja 3 a Edo
An gano cewa, suna aiki ne a gonakin kamfanin lokacin da ’yan bindigar suka fito daga cikin daji suka kashe su
Rahotanni sun ce wasu ’yan bindiga sun kashe ma’aikatan kamfanin manja na Okomu Oil guds uku a lokacin da suke aiki a cikin gonar kamfanin a Benin, jihar Edo.
An gano cewa ma’aikatan suna tsaka da aiki ne ’yan bindigar suka fito daga cikin daji suka kashe su a ranar Litinin Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a unguwar Okumu da ke Ƙaramar hukumar Onia ta Kudu maso Gabas ta jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Fidelis Olise, ya ce an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda kuma an fara bincike kan lamarin.
“Zan iya tabbatar muku da cewa ‘yan bindiga sun kashe ma’aikatanmu uku a ranar Litinin yayin da suke aiki a gonar,” in ji shi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin dakile sake aukuwar harin.
“Waɗanda suka kai harin sun fito ne daga wata jiha mai maƙwabtaka da su kuma ana kokarin kama maharan domin gurfanar da su a gaban kotu.
“Bincike na farko ya nuna cewa ’yan bindigar sun fito ne daga rafi a jihar da ke maƙwabtaka da su, wanda ba zan so in ambata ba. Harin yana da ban tsoro,” in ji shi.
Kwamishinan ya kuma ce ’yan sanda na aiki tare da hukumomin Okomu don tabbatar da hanyoyin da za a samu muhallin da ma’aikata a kowane lokaci za su samu natsuwa.