‘Yan bindiga sun kashe mafarauta 5 a kauyen Adamawa

Wasu ‘yan bindiga akan rakuma sun kashe mafarauta biyar a yankin Gombi cikin jihar Adamawa. Wani mazaunin unguwar ya sanarwa majiyarmu cewa, maharan sun kaiwa mafarautan hari ne a ranar Juma’a kusa da kauyen Zumo da ke yankin Arewa maso Gabas na jihar. Wani mafarauci da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, wadanda suka […]

‘Yan bindiga sun kashe mafarauta 5 a kauyen Adamawa

Wasu ‘yan bindiga akan rakuma sun kashe mafarauta biyar a yankin Gombi cikin jihar Adamawa. Wani mazaunin unguwar ya sanarwa majiyarmu cewa, maharan sun kaiwa mafarautan hari ne a ranar Juma’a kusa da kauyen Zumo da ke yankin Arewa maso Gabas na jihar.

Wani mafarauci da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, wadanda suka kashe mafarautan ‘yan Boko Haram ne da suke shirin afkawa jami’an tsaro da ‘yan bangan yankin.

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yan sanda jihar Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da kai harin kuma ya ce a yanzu haka sun tura jami’in ‘yan sandan yankin.