’Yan bindiga sun kashe magidanci da ’yarsa a Sakkwato
Mazauna sun ce maharan sun kwashe kusan awa guda suna ta’asa kafin jami’an tsaro su iso.
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da kusan mutum 17 yayin wani da suka kai hari a ƙauyen Garin Faji da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
Mazauna sun ce maharan sun biyo dare inda suka shigo ƙauyen a ƙafa suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
- Matar da ta jagoranci ɗaga ɗan kamfai ta samu muƙami a Kano
- Datti Baba-Ahmed ya yanki katin jam’iyyar PRP
Daga bisani sun shiga wani gida inda suka kashe wani mai gidan, Haruna Dan Kwambo da ’yarsa ’yar kimanin shekara takwas, sannan suka yi awon gaba da matansa da na na ’yan uwansa da ’ya’yansu.
Bayanai sun ce waɗanda aka yi awon gaba da su sun kai 17, yawancinsu mata da yara, yayin da suka kwashe shanu kusan 50.
Mazauna sun ce maharan sun kwashe kusan awa guda suna ta’asa kafin jami’an tsaro su iso.
Kazalika, sun ce wannan ba shi ne farau ba domin kuwa a kwannan baya wani harin ’yan bindigar ya tilasta wa mazauna tserewa, inda kuma aka yi rashin sa’a kwale-kwale ya kife da wasu mutum 10 da ke neman tsira.
Sun roƙi gwamnati da ta gaggauta ceto waɗanda aka sace, suna mai cewa halin da suke ciki ya yi tsanani.
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufai amma kuma haƙarta ba ta cimma ruwa ba har zuwa hada wannan rahoto.