’Yan bindiga sun kashe mai unguwa sun kuma sace tsohon kansila a Nasarawa

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kashe mai Ungwar Mada da ke karamar Hukumar Kokona a Jihar Nasarawa Malam Saleh Tanko tare da sace wani tsohon kansila mai suna Micah Dogo, sannan suka yi fyade ga wata matar aure a kauyen. Sarkin Garaku Abaga Toni Silbester Ayih ne […]

’Yan bindiga sun kashe mai unguwa sun kuma sace tsohon kansila a Nasarawa

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar NasarawaWasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kashe mai Ungwar Mada da ke karamar Hukumar Kokona a Jihar Nasarawa Malam Saleh Tanko tare da sace wani tsohon kansila mai suna Micah Dogo, sannan suka yi fyade ga wata matar aure a kauyen.
Sarkin Garaku Abaga Toni Silbester Ayih ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai kan aukuwar lamarin a fadarsa da ke Garaku hedikwatar karamar hukumar a karshen mako jiya. Basaraken ya ce “Da misalin karfe 1:00 na dare ne ’yan bindigar masu yawa da ba a san inda suka fito ba dauke da miyagun makamai suka shiga Unguwar Mada inda suka wuce gidan Mai ungwa Malam Saleh Tanko suka bude masa wuta a kahon zuciyarsa a gaban iyalansa ya mutu nan take. Daga nan suka wuce gidan wani tsohon kansila mai suna Micah Dogo suka kama shi. Da suke fitowa daga gidan tsohon kansilan ne sai suka gamu da wata matar aure suka yi lalata da ita.”
Abaga Toni Silbesta Ayih ya kara da cewa washegari ’yan bangar da ke tsintiri a kauyen sun kama wani Bafulatani da ake zargin daya ne daga cikin wadanda suka aikata wannan danyen aiki. Ya ce wanda ake zargin ’yan banga sun kama shi ne da bindiga kirar AK47 rataye a wuyansa da wasu layu.
Ya ci gaba da cewa “Da ’yan bangar suka tsayar da shi don su caje shi sai ya ki amincewa da haka. Daga nan sai suka kama shi suka kada shi. Da suka caje jikinsa sai suka gano bindigar da layun.” Ya ce tuni ’yan bangar suka mika wanda ake zargin ga ’yan sanda domin daukar mataki da ya dace.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Cornelius Ocholi ya tabbatar wa wakilinmu aukuwar lamarin inda ya ce lallai wasu ’yan bindiga da muke tunanin ’yan fashi ne sun kashe Mai Ungwar Mada sun kuma sace wani mutum a kauyen. Ya ce tuni rundunar ta soma gudanar da bincike don kamo wadanda suka yi danyen aikin. Kuma ta turo jami’anta da dama zuwa kauyen don hana aukuwar lamarin nan gaba.