’Yan bindiga sun kashe manoma 14 a Ondo
Ina tsammanin zuwa yanzu sun kashe mutum fiye da 40 a ƙauyukan yayin da wasu da dama sun jikkata.

’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo.
Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne.
Wata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu.
Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan da abin ya shafa da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce har kawo yanzu wasu daga mutanensu da suka tsere cikin jeji ba su dawo ba.
Ya ce tun a ranar Litinin ta makon jiya aka soma kawo musu hari, sai dai mafi munin ciki shi ne wanda ya auku a ranar Juma’a ba tare da maharan sun fuskanci wata tirjiya ba.
“Tun cikin daren ranar Juma’a suka soma kawo mana kuma duk wanda suka gani sai su buɗe masa wuta.
“Mutanenmu da dama sun gudu neman mafaka a jeji kuma ina tsammanin zuwa yanzu sun kashe mutum fiye da 40 a ƙauyukan yayin da wasu da dama sun jikkata.”
Da take zantawa da Aminiya ta wayar tarho, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisamya, ta tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarta, an soma gudanar da bincike kan lamarin wanda kawo yanzu an tsinto gawawwakin mutum 14 a jeji.
Ta ce an tura tawagar jami’an ’yan sanda da za ta bi sawun ɓata-garin kuma tuni tarzoma ta lafa a yankin.