’Yan bindiga sun kashe manoma 4, sun sace 12 a Sakkwato

Suna tsaka aiki ne ’yan bindigar suka afka musu. Kuma nan take suka harbe manoma huɗu suka mutu.

’Yan bindiga sun kashe manoma 4, sun sace 12 a Sakkwato

’Yan bindiga ne sun kashe manoma huɗu tare da sace aƙalla mutum 12 a wani hari da suka kai da rana tsaka a gundumar Gandi da ke Ƙaramar Hukumar Rabah a Jihar Sakkwato.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na safiyar ranar Talata yayin da waɗanda abin ya shafa ke gudanar da ayyukansu na noma a gonakinsu da ke bayan gari.

Da yake tabbatar da aukuwar harin, wani mazaunin Gandi, Malam Tukur Muhammad, ya ce lamarin ya faru ne a gonarsa, wadda ya daina nomawa saboda matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin.

“Gonata ce aka kai harin. Saboda tana wajen gari, na daina nomanta. Sai dai wasu ’yan uwana sun nemi izinina za su yi amfani da ita, kuma na amince,” in ji shi.

“Suna tsaka aiki ne ’yan bindigar suka afka musu. Kuma nan take suka harbe manoma huɗu suka mutu, sannan suka yi awon gaba da wasu da dama da ke aiki a wurin,”in ji shi.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce akwai yiwuwar harin ya faru tun wajen ƙarfe 9 na safe, amma jama’ar gari ba su gano hakan ba sai da misalin ƙarfe 11.

“Mun shiga tsananin fargaba saboda babu wanda ke cikin aminci a gabashin Jihar Sakkwato,” in ji shi.

Wani jami’in rundunar tsaron gandun daji da ke Sakkwato da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa an gano mutum 12 daga cikin waɗanda aka sace.

“Mun dawo ne daga wurin da lamarin ya faru. An kashe manoma huɗu, yayin da wani ya samu raunukan harbin bindiga kuma yanzu haka yana karɓar magani a asibiti.

“Ya zuwa yanzu, mun tabbatar da cewa mutum 12 ne aka yi garkuwa da su,” in ji jami’in.

Sai dai wani jami’in tsaro ya bayyana cewa dakarun rundunar Operation FANSAN YAMMA sun yi nasarar ceto mutum bakwai daga cikin waɗanda aka sace bayan sun yi artabu da ’yan bindigar.

Majiyar ta ce sojojin sun kai ɗauki cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya har jami’an suka samu damar ceto waɗanda aka sace.

Majiyar ta ƙara da cewa wani farar hula ya samu raunin harbin bindiga a lokacin harin, inda aka garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Gandi domin kula da lafiyarsa.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce har zuwa lokacin bai samu rahoton aukuwar lamarin ba, amma ya yi alƙawarin tuntubar jami’in ’yan sanda mai kula da yankin domin samun cikakkun bayanai.

Wannan hari na ƙara nuna irin ƙalubalen tsaro da al’ummomin gabashin Sakkwato ke fuskanta, inda hare-haren ’yan bindiga, kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane suka zama ruwan dare a yankin.