’Yan bindiga sun kashe manoma 9 sun yi garkuwa da gommai a Kaduna
Wasu manoman ƙauyen sun yi yunƙurin kashe wani ɗan bindiga da ya yi yunkurin kai musu hari.
Wasu manoma tara sun riga mu gidan gaskiya, yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama, bayan da ’yan bindiga sun kai hari wani ƙauye a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kai harin ne ranar Asabar a gonakin da ke wajen ƙauyen Kakangi, inda suka buɗe wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta.
- Bayanan IMF kan zargin kashe N8.8trn a ɓoye ya tayar da ƙura a Najeriya
- Tsananin zafi ya haddasa tashin gobarar daji a ƙasashen Turai shida
Wannan lamari ya yi sanadin mutuwar mutum tara, sannan daga bisani maharan suka yi awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba kawo yanzu.
Wani rahoton tsaro da aka shirya wa Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce an gano gawarwaki tara zuwa yanzu, yayin da hukumomin yankin suka tabbatar da gano shida daga cikinsu.
Rahoton ya nuna cewa maharan na kai hare-hare musamman kan kauyukan da suka bijire wa umarnin ’yan bindiga na biyan harajin da suke tilasta wa mazauna yankunan.
Sai dai wani jagoran al’umma a Birnin Gwari, Kabiru Ishaq, ya ce mutum goma ne aka kashe a harin.
A cewarsa, harin ramuwar gayya ne bayan wasu manoma sun yi yunƙurin kashe wani ɗan bindiga da ya yi yunkurin kai musu hari a wannan ranar.
Rahoton ya ce ɗan bindigar da ya tsira ya koma ya dawo da ƙarin mayaƙa, inda suka kai farmaki domin ɗaukar fansa.
A baya dai, an yi ƙoƙarin samar da zaman lafiya tsakanin al’ummomin Birnin Gwari da ’yan bindiga, bayan wata yarjejeniya da aka cimma a watan Nuwamban 2024, amma hare-haren sun ci gaba da aukuwa.
A watan da ya gabata ma, an kashe aƙalla manoma shida, yayin da aka sace wasu 20 a wani hari da aka kai ƙauyen Danauta da ke wannan yanki.
Jihar Kaduna na ci gaba da kasancewa cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga, musamman a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Chikun da kuma Kajuru.