’Yan bindiga sun kashe matafiya 10 a Zamfara
“’Yan bindigar sun kai hari kan jami’an tsaron da ke rakiyar matafiyan a hanyarsu ta zuwa Ɗansadau. Sun kashe wasu jami’an tsaro da fararen hula da kuma mambobin kungiyar CJTF, yayin da wasu da dama suka samu raunuka,” in ji shi
‘Yan bindiga sun kashe basarake a jihar Kebbi
’Yan bindiga sun kai hari kan ayarin matafiya a Jihar Zamfara, inda suka kashe aƙalla mutum 10 tare da jikkata wasu da dama.
Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi a kan hanyar Magami zuwa Ɗansadau, inda ya tilasta wa matafiya da dama tserewa zuwa cikin daji domin neman tsira.
Wani ganau mai suna Malam Aliyu ya ce yankin Dogon Santsi na buƙatar tsauraran matakan tsaro saboda yawaitar hare-haren ’yan bindiga a yankin.
Ya bayyana cewa, “Mutane sun shafe sa’o’i da dama suna jiran jami’an tsaro su yi musu rakiya kafin daga baya a kawo harin,” in ji shi.
- Yadda tsohon ɗan Majalisar Tarayya daga Jigawa ya rasu a hannun ’yan bindiga
- Katsina ta karrama gwarazan ɗalibai da kyautar sabbin motoci
Ya ce ’yan bindigar sun kai wa ayarin hari ne yayin da jami’an tsaro ke raka matafiya zuwa Ɗansadau.
“’Yan bindigar sun kai hari kan jami’an tsaron da ke rakiyar matafiyan a hanyarsu ta zuwa Ɗansadau. Sun kashe wasu jami’an tsaro da fararen hula da kuma mambobin kungiyar CJTF, yayin da wasu da dama suka samu raunuka,” in ji shi.
Aliyu ya ƙara da cewa an tabbatar da mutuwar mutum 10, yayin da ake ci gaba da neman wasu da ba a gan su ba.
“Mun tabbatar da mutuwar mutum 10, amma har yanzu ana ci gaba da neman wasu,” kamar yadda ya bayyana.
Wani matafiyi mai suna Aminu Muhammad ya ce waɗanda suka tsira sun jira ƙarin jami’an tsaro kafin a samu damar kai waɗanda suka jikkata zuwa Gusau domin samun kulawa.
Aminu ya kuma yi zargin cewa ’yan bindigar sun yi garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance yawansu ba yayin harin.
Sai dai ya yaba wa jami’an tsaro kan kokarin da suke yi wajen kare matafiya.
Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara bai yi nasara ba, domin kakakin rundunar, Yazid Abubakar, bai amsa saƙon da aka tura masa na neman ƙarin bayani ba, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto.