’Yan bindiga sun kashe mutane 8 a Binuwe

Rahotanni sun ce adadin waɗanda aka kashe a jerin hare-haren da aka fara tun ranar Juma’a har zuwa da safiyar Lahadi ya kai 18.

’Yan bindiga sun kashe mutane 8 a Binuwe

’Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum takwas tare da jikkata wasu biyar a wani hari da suka kai ƙauyen Otukpo-Nobi da ke Ƙaramar Hukumar Otukpo a Jihar Binuwe. 

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, Udeme Edet, ya tabbatar da harin, inda ya ce mutum takwas ne suka mutu.

Sai dai wasu rahotanni sun ce adadin waɗanda aka kashe a jerin hare-haren da aka fara tun ranar Juma’a har zuwa da safiyar Lahadi ya kai 18.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya danganta lamarin da kisan wani shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani da aka yi makonni biyu da suka gabata.

Sai dai Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) reshen Jihar Binuwe ta musanta hannu a lamarin, tana mai Allah wadai da hare-haren.

Har zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, yayin da mata da matasa suka gudanar da zanga-zanga a Otukpo domin nuna adawa da kashe-kashen.