’Yan bindiga sun kashe mutane da yawa a kauyukan Katsina

An kashe jama’a da dama a harin da ‘yan bindiga suka kai kauyuka biyu a Karamar Hukumar Batsari da ke jihar Katsina. Rahoton ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga garuruwan Dankar da Tsauwa da misalign karfe 8:30 na dare, inda suka yi harbi suna kone gidajen jama’a da motoci. Mazauna garin sun yi ta […]

’Yan bindiga sun kashe mutane da yawa a kauyukan Katsina

An kashe jama’a da dama a harin da ‘yan bindiga suka kai kauyuka biyu a Karamar Hukumar Batsari da ke jihar Katsina.

Rahoton ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga garuruwan Dankar da Tsauwa da misalign karfe 8:30 na dare, inda suka yi harbi suna kone gidajen jama’a da motoci.

Mazauna garin sun yi ta hijira zuwa cikin garin Karamar Hukumar Batagarawa da ke jihar don tsira da rayukansu.

Kakakin rundunar  ’yan sandan jihar SP Gambo Isah, ya ce nan gaba kadan za su yi bayani game da harin da aka kai.