’Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Kamaru

Maharan sun kuma jikkata wasu mutum 2 a harin

’Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Kamaru

Wasu masu fafutukar kafa kasar Ambazoniya a Kamaru

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum 10 tare da jikkata wasu biyu a wani titi da ke birnin Bamenda na Arewa maso Yammacin Kamaru mai fama da rikici, kamar yadda Gwamnan Jihar ya tabbatar.

Wani ganau a yankin ya ce maharan sun isa wajen ne a kan motoci da yammacin Asabar, inda suka bukaci mutane su kwakkwanta a kasa saboda sun ki goyon bayan kungiyoyi masu son ballewa daga kasar.

Daga nan ne kuma suka bude wa mutanen wuta, inda wasu suka tsaya, wasu kuma suka ranta a na kare.

Babbar kungiyar ’yan tawayen ADF da ke fafutukar kafa kasar Ambazoniya a yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi ce dai take fada da gwamnati tun a shekara ta 2017, bisa zargin nuna mata wariya daga gwamnatin kasar mai rinjaye wacce ke amfani da Faransanci.

Gwamnan Yankin Arewa maso Yammacin Kasar, Adolphe Lele Lafrique, ya ce tuni suka kaddamar da bincike domin gano wadanda suka kai harin.

“Za mu kama ’yan ta’addan da suka kai wannan harin. Yanzu haka mun fara bincike, kuma za mu fitar da sanarwa a kan haka yau zuwa anjima.”

Wani ganau ya ce maharan sun isa wajen ne a cikin kayan sojoji, sannan sun mamaye mahadar Nacho da ke birnin, wanda ke dauke da shagunan sayar da abinci da wuraren shan giya da kantuna, wajen karfe 7:30 na yamma.

Sama da mutum 6,000 ne dai aka hallaka tun lokacin da aka fara zanga-zangar nuna rashin amincewa a yankin da ke amfani da Ingilishi tun a shekara ra 2017.

Ko a farkon wannan tanat sai da kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta Amnesty International ta soki lamirin dakarun gwamnatin kasar da na ’yan tawaye da aikata kashe-kashe da fyade da kone gidaje da kuma azabtar da mutane a yankin na Kamaru.

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899