‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a kauyukan Katsina

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 10 a kauyukan Gobirawa  da Sabawa da ke karamar hukumar Safana a jihar  Katsina bayan wani farmaki da suka kauyukan. Jama’ar kauyen sun ta tura sakonnin neman agaji lokacin da ‘yan bindigar suka yi wa kauyen kawanya da babura a daren jiya Talata. Mai magana da yawun hukumar ‘yan […]

‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a kauyukan Katsina

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 10 a kauyukan Gobirawa  da Sabawa da ke karamar hukumar Safana a jihar  Katsina bayan wani farmaki da suka kauyukan.

Jama’ar kauyen sun ta tura sakonnin neman agaji lokacin da ‘yan bindigar suka yi wa kauyen kawanya da babura a daren jiya Talata.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah da misalin karfe 6:10 na Yamma wasu tawagar ‘yan bindiga da suka kai sama da mutum 150 a babura sun kaiwa kauyukan hari, sun kuma kashe mutum 10.